Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Zasu Rika Sa Ido A Kan Makarantun Mata Na Arewa Maso Gabas


Sabon ofishin rundunar sojin Najeriya dake jihar Neja
Sabon ofishin rundunar sojin Najeriya dake jihar Neja

Biyo bayan sace 'yan matan makarantar sakandare ta Dapchi dake jihar Yobe da wadanda ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne suka yi, yanzu rundunar sojojin Najeriya ta kuduri aniyar sa ido a kan duk makarantun sakandare na mata dake yankin arewa maso gabashin kasar

Rundunar sojin Najeriya ta ce zata rika sa idanu sosai a makarantun sakandare na mata dake yankin arewa maso gabashin kasar domin tabbatar da tsaro a kansu.

Wannan sanarwar na zuwa ne a daidai lokacin da ake kokarin sanin makomar yaran makarantar sakandare ta mata dake Dapchi cikin jihar Yobe da wasu da ake kyautata zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne suka sace cikin makon jiya.

Yayinda yake bude wani sabon ofishin sojojin da wajen ba da horo a barikin sojojin dake Kwantagora daraktan ayyuka da ba da horo na rundunar sojin Najeriya Manjo Janar David D Ahmadu ya ce kodayake aikin tsaro a makarantun na 'yan sanda ne da sauran jami'an tsaro amma hakan ba zai hanasu sanya idanu a makarantun ba.

Manjo Janar David D Ahmadu wanda ya wakilci hafsan hafsoshin sojojin Janar Tukur Yusuf Buratai ya bukaci hadin kan 'yan jarida da jama'ar gari musamman a yakin da suke yi da 'yan ta'adda.

Acewar Janar Ahmadu 'yan jarida ya kamata suna fadin gaskiyar abun da ya faru. Ya kira 'yan jarida su dinga ba da labarin da zai kai ga cafke masu tada zaune tsaye a kasar.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:42 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG