Taron kollin tsaro na kasa ya samu halarcin shugaban kasa Muhammadu Buhari, gwamnoni 36, tare da tsofaffin shugabanin kasa, da ya kuma hada da alkalin alkalai, kana shugaban majalisar dattawa da na wakilai.
Gwamnan jihar Jigawa Abubakar Badaru, ya zanta da manema labarai, inda ya bayyana abubuwan da suka tattauna akai, da suka hada da matsalar tsaro, da ta shafi satar jama’a da garkuwa da su, da rikici tsakanin manoma da makiyaya, haka kuma da matsalar tsagerun Naija Delta.
Ya bayyana cewar mai ba shugaban kasa shawara a harkar tsaro ya kwashe tsawon lokaci yana gabatar da bayanan matakin da suke dauka, da kuma shawarwari da masana harkar tsaso su ke badawa don ganin an magance matsalar a kowane mataki.
A cikin jawaban da aka tattauna, an karfafa magana akan matsalar yadda ake ma Fulani kallon wadanda ba ‘yan kasa ba, bayan sun kwashe shekaru a yankunan da suke, wannan shima matsala ce da su ka tatauna yadda za’a bullo da hanyar magance ta.
A karshe dai taron ya tattauna kan hanyoyin da za a bi don kyautata danganta tsakanin ‘yan kasa na kowane yanki, kabila, da addinai, da mutunta juna, kana an dauki matsaya daya da ta shafi tattalin arzikin kasa.
Facebook Forum