A kokarin kawar da rikice rikice da samar da dawamammen zaman lafiya tsakanin makiyaya da manoma a Oyo, gwamnatin jihar ta ce za ta kafa wata hukuma ta musamman da za ta sa ido ga harkokin bangarorin biyu.
Gwamnan jihar Sanata Abiola Ajimobi ya sanar da hakan a Ibadan babban birnin jihar a lokacin taron masu ruwa da tsaki a kiwo da noma da jami'an tsaro.
Gwamnan ya ce wajibi ne a kafa hukumar da za ta sanya ido lokaci zuwa lokaci ana zagayawa a duk fadin jihar domin tabbatar da cewa babu masu aikata laifuka kamar sace mutane ko sace shanu dake fakewa da sunan su makiyaya ne.
A cewar gwamnan za'a yiwa makiyaya da dabbobinsu rajista kuma duk makiyayin da aka kama dauke da makami za'a hukumtashi. Kazalika gwamnan ya tabbatar da aniyar gwamnatinsa na samar wa makiyaya wurin kiwo domin wanzar da zaman lafiya tsakanin makiyaya da manoma.
Shi ma kwamishanan 'yan sandan jihar ya ce rikicin makiyaya da manoma da ya auku makwanni biyu da suka gabata ya yi sanadiyar mutuwar mutane tara. Ya kira jama'a da su rungumi zaman lafiya su daina kashe kansu. Injishi jami'an tsaro zasu yi aikinsu babu tsoro babu ja da baya.
Ga rahoton Hassan Umaru Tambuwal da karin bayani.
Bangarorin makiyaya da manoma su ma sun nemi da a zauna lafiya kana sun yiwa gwamnatin jihar Oyo godiya akan hada taron neman zaman lafiya tsakaninsu.
Facebook Forum