Kakakin rudunar ‘yan sandan Abdullahi Jimo, ya ce sunyi bincike da ingantaccen izini, kuma cikin abin da suka gano har da fiyel-fiyel da suka shafi harkokin kudi a jihar Gombe tun shekara ta 2005.
Haka kuma an gano wani fiyel mai kunshe da bayanai kamar yadda rundunar ta ce, tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau, ya kitsa hallaka marigayi Sheikh Ja’afar Muhd Adam.
Sanata Goje, wanda tun farko ya ce akwai takardun bayanan kasafin kudin bana da ‘yan Sanda suka yi awon gaba da su, ya bayar da tabbacin dawo da kayan.
Sai dai kuma Sanata Goje ya yi watsi da labarin samun fiyel ko wata takarda kan kashe Mallam Ja’afar, inda ya ce bashi da wata alaka da wata takarda da ta shafi yadda wai shekarau ya kitsa kashe Sheikh Ja’afar. Har ma ya bada missalin cewa lokacin da aka yi kisan shi yana Gombe yana Gwamna na jam’iyyar PDP kuma Shekarau yana Gwamna a Kano karkarin jam’iyyar ANPP.
Goje dai bai fadi ko wanne irin mataki zai ‘dauka ba, bayan wannan kazafi da ya ce rundunar ‘yan sandan Najeriya ke kokarin masa.
Domin karin bayani ga rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.
Facebook Forum