Shugaba Trump ya bayyana cewa 'yan hamayya na jam'iyyar Democrat ne suke fakewa da haka, domin su jingina faduwar zaben shugaban Amurka da suka yi.
A kalamai da yayi ta Twitter yau Talata, Trump yace bayanai kan binciken dangantaka tsakanin hadimansa da jami'an Rasha da zummar taimaka masa ya ci zabe, yanzu ya sha kan "kafofin yada karya," kalaman da yake amfani da su wajen kiran kafofin yada labaran Amurka.
Tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton, wacce Trump ya kada a zaben, tana aza laifin faduwarta kan katsalandar da Rasha tayi a zaben.
Da yake magana kan wannan batu, dan majalisar dattijan Amurka John McCain , jiya Litinin yace a ganinsa, Rasha da shugabanta Vladimir Putin, sune "kalubale mafi tsanani" da Amurka take fuskanta fiye da ma kungiyar ISIS.
Da yake magana lokacinda yake ziyara a Australia, McCain, ya gayawa gidan rediyon kasar cewa, Rasha tayi kokarin ta "lalata ginshikin demokuradiyya" a kokarin da tayi na katsalanda a zaben shugaban Amurka, da kuma irin haka da kasar tayi a wasu sassan duniya.
Facebook Forum