Kungiyar mayakan al-Shabab ta kaddar da jerin hare-hare tun daga ranar Asabar, wadanda su ka yi sanadin mutuwar mutane akalla 17 a Somaliya.
Hukumomin yankin Lower Shabelle sun fada wa Sashen Somaliyanci na Muryar Amurka cewa ‘yan bindigar sun kai hari a kauyen Qoryoley a ranar Asabar da daddare, inda suka yi amfani da makamin roka da kuma manyan bindigogi, inda suka hallaka mutane 9.
Magajin garin Qoryoley, Sayid Ali Ibrahim, ya fada wa Sashen Somaliyanci na Muryar Amurka cewa makamin rokar da yan bindigar suka harba shi ne ya yi sanadin yawancin mace-macen da aka samu.
Sojojin gwamantin Somaliya tare da taimako daga dakarun kungiyar hadin kan Afrika (wato AU), wadanda ske da sansani a bayan garin, sun dakile harin, a cewar jami’ai.
Sai dai wasu mazauna Qoryoley zun yi zargin cewa harba manyan makamai da dakarun AU su ka yi ne ya janyo mutuwar wasu fararen hula.
Facebook Forum