WASHINGTON D.C. —
Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya zargi Iran da jagorantar kai wadannan hare-hare a kasar ta Saudiyya, lamarin da ya sa adadin man da take fitarwa a rana ya ragu matuka.
Sai dai Pompeo ya tsame hannun Yemen a harin, yana mai cewa hukumomin Tehran ne ke da alhaki
Duk da cewa, mayakan na Houthi sun dauki alhakin kai harin, Sakataren harkokin wajen na Amurka, ya shiga shafinsa na Twitter ya wallafa cewa, “babu shaidar da za ta nuna cewa hare-haren daga Yemen ne.”
Pompeo ya kuma yi kira ga kasashen duniya da su fito fili su yi Allah wadai da wannan danyan aiki da Iran ta yi.