WASHINGTON D C —
Masu kada kuri’a a kasar Tunisia sun fara zuwa rumfunan zabe yau Lahadi don zaben sabon shugaban kasarsu.
‘Yan takara kusan 26, daga jam’iyyu daban daban ne suke akan takardar zaben a wannan karon.
Wannan ne karo na biyu da ake zaben shugaban kasa a karkashin tsarin dimokradiyya a kasar.
Rashin habbakar tattalin arziki da kuma karuwar rashin ayyuka a kasar, su ne abubuwan da ke tuni da cewa juyin juya halin da aka yi a Tunisia, wanda aka yiwa lakabi da "Jasmine" shekaru 8 da suka gabata, haka ba ta cimma ruwa ba.
Akwai yiwuwar sake yin zaben shugaban kasar.
Bayan mutuwar shugaban Tunisia Beji Caid Essebsi a watan Yulin da ya gabata ne aka yanke shawarar yin zaben na yau Lahadi.
Facebook Forum