Suma daliban sun koka akan rashin samun wasu alawus alawus din su kamar yadda wani daga cikin daliban ya bayyana cewar ana nuna masu bambanci domin a cewar sa, an fara biyan wasu jami’o’in, amma har yanzu basu gani a kasa ba.
Daliban sun aika wa gwamnatin kasar da sakon cewa sun zo makarantar ne domin neman ilimi ba barci ba, dan haka suna kira da a gaggauta biyan su alawus alawus din su kuma a biya malamai domin su koma su cigaba da gudanar da ayyukan su akamr yadda suka saba.
Malam muntari Usman shine shugaban majalisar mashawarta ta da’irar jihar Damagaran, ya yi alkawarin kamawa domin tabbatar da magance matsalar domin a cewar sa, matsala ce data shafi kowa.