Taron nada manufar kirkiro masalaha ta hanyar gudanar da ayyuka na zahiri.
Onarebul Baraka Yusuf shugaban kungiyar 'yan majalisa masu yaki da talauci shi ya shaidawa Muryar Amurka manufar taron. Yace talauci kam akwaishi. Suna son su gano irin matakan da ya kamata su dauka domin shawo kansa.
Lokacin kaka ana samun cimmaka a karkara sai mutane su bannatar dashi. Yakamata a wayewa mutane kai akan abunbuwan da yakamata su yi domin su tanadi abincin. Tafiya barkatai da mutane keyi saboda talauci idan an waye masu kai zasu daina.
Shugaban wata kungiya Malam Musa Changari yace la'akari da yunkurin da wasu 'yan majalisa suka yi domin taimakawa talakawa ya sa kungiyarsa ta hada kai dasu a wannan tafiya. Sun gane 'yan majalisa na iya sa ayi dokar da zata kare talakawa daga yunwa.
Dan majalisa Murtala Alhaji Mamuda yace sun hadu ne su fuskanci lamarin domin a kawo masalaha musamman tunda suna da goyon bayan 'yan majalisa dukansu. Zasu duba fannin noma da zaman lafiya da duk sauran fannonin.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.