Gwmanonin jihohin ukku da suka hada da Yaounde da Douala da Linda suka rabtaba hannu kan yarjejeniyar sayo motocin daga kasar Portugal saboda gudanar da zirga zirga a cikin manyan biranen jihohin ukku.
Jihohin sun sayi motocin ne domin samar ma al'ummarsu saukin yin zirga zirga, musamman ma a cikin gari. Motocin zasu taimaka a lokacin gasar kwallon kafa na mata na nahiyar Afirka da za'a yi cikin biranen jihohin ukku..
Dangane da gyaran motocin, yarjejeniyar ta kunshi aikawa da makanikan kasar zuwa kasar Portugal domin su koyo yadda ake gyara motocin. Kamfanin dake Portugal zai samar da kayan gyara.
Muhammad Buba mai kula da motocin a jihar Douala yace motocin zasu zo da kayan da za'a canza masu idan sun baci.
To saidai wani Alhaji Abatcha ya kushewa shirin, lamarin da yace ya basu mamaki domin wai, sun saba da yin anfani da motocin Faransa da Amurka ko Japan. Kasar Portugal bata yi fice a kiran motoci ba kuma idan ba kudi ake son a wawure ba sayan motoci daga Portugal bashi da wani anfani.
Ga rahoton Garba Awal da karin bayani.