Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Boko Haram Na Samun Sabbin Mayakan ISIS daga Tunisia


Wani shugaban kungiyar Boko Haram
Wani shugaban kungiyar Boko Haram

Ministan tsaro na Tunisia Farhat Hachani, yana kashedin cewa mayakan kungiyar ISIS wadanda ake tasa keyarsa daga tungoginsu a Sirte na Libya, sun nufi kudu suna shiga Boko Haram, wasu kuma sunyi yamma inda zasu yi barazana ga yankin dake arewacin Afirka.

Da yake magana a wani taro kan batun tsaro jiyaTalata a birnin Paris, Farhat yace kimanin 'yan kasar Tunisia dubu sun shiga kungioyi daban daban dake ikirarin suna jihadi, kuma da irin koma bayan da kungiyar ISIS take samu a baya bayan nan, suna iya komawa kasar, kuma babu wani shiri na tunkarar irinsu a arewacin Afirka.

Rahotanni da kafofin yada labarai ciki harda da AFP, da Reuters, sun ce duk da hasarar yankuna da suke karkashinta, kungiyar ISIS tana ci gaba da samun sabbin magoya baya, da samun makamai, kuma tana ci gaba da kaddamar da hare haren ta'adanci a fadin duniya.

A wani sharhi da ya gudanar, kamfanin dillancin labarai na Reuters, yace kungiyar ISIS tana kaddamar da sabbin hare haren ta'addanci cikin kasa na kwanaki hudu kowane mako daga watan Yunin bana zuwa yanzu.

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG