Sai dai masana kimiyya na cewa, abu ne mawuyaci dokar rage shekarun tsayawa takarar zaben ta yi tasirin da ake bukata.
Dokar wadda ke cikin jerin dokoki fiye 10 da Majalisar dokoki ta kasa ta mikawa shugaban domin rattaba hannu, ta rage mafi karancin shekarun dantakar shugaban kasa daga 40 zuwa 35 dan takarar gwamna daga shekaru 35 zuwa 30 yayin da mafi karancin shekarun dan takarar Majalisar dokoki ta kasa dana jihohi zai kasance 25.
Yanzu haka dai matasan na bayyana farin ciki dangane da wannan alkawari na shugaba Buhari na sanya hannu akan wannan doka, Kwamrad Kabiru Sa’idu Dakata, na daga cikin matasan da sukayi gangami a kwanakin baya domin matsa lamba domin ganin shugaba Buhari ya sanya hannu akan wannan doka.
Tuni dai masana kimiyyar siyasa ke fashin baki game da tasiri da wannan doka ka iya yi a tsarin siyasa Najeriya ko akasin haka, Dakta Sa’idu Ahmad Dukawa malami ne a Jami’ar Bayero Kano.
Haka zalika Dr Sa’idu Dukawa ya yi Karin haske dangane da matakan daya kamata a dauka ta yadda matasa ka iya samun damar taka rawa a fagen siyasar Najeriya.
Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.
Facebook Forum