Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jama'a Sun Bayyana Ra'ayoyin Su Kan Mulkin Dimokradiyya A Najeriya


'Yan Najeriya
'Yan Najeriya

Ra'ayoyin 'yan Najeriya sun banbanta dangane da ci gaban da aka samu karkashinmulkin dimokradiyya.

Wasu ‘yan Najeriya na ganin cewa, shekaru 19 na mulkin damokaradiyya ba tare da yankewa ba shi kansa wani ci gaba ne da kasar ba ta taba samu ba a tarihi.

Yayin da kuma hakan ya haifar da wasu al'amura na ci gaba a wani fannin, wasu sun ce dimokradiyyar Najeriya ta yi dama domin an samun ci gaba kwarai, inda yake akwai 'yanci da mutum da zai fadi abinda yake bukatar fadi sannan akwai wasu abubuwan ci gaba da gwamnati ke yi.

Sai dai kuma wasu sun ce sha'anin yaki da cin hanci da rashawa da kuma tabarbarewar tsaro na daga cikin muhimman al'amuran da ke jan hankalin ‘yan Najeriya inda ake samun ra'ayoyi mabanbanta dangane da nasara ko akasin haka a kasar.

Wasu na ganin cewa an samu ci gaban mai hakar rijiya ga abinda ya shafi tsaron domin abubuwan da ke faruwa yanzu babu su a da kamar Boko haram da sace-sacen mutane. Wadannan abubuwan ba karamin ci baya ba ne ga dimokradiyya ba.

Barrista Mu'azu Yabo ya ce rashin gudanar da mulkin dimokradiyya tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnatin jihohi da ma kananan hukumomi kamar wanda tsarin mulki ya zo da shi na cikin manyan matsalololin da dimokradiyya ke fuskanta.

A yayin da kuma wasu ke cewa an fara cika alkawuran da gwamnatin APC ta dauka a yayin yakin neman zaben ta.

Saurari ra'ayoyin

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:55 0:00

Facebook Forum

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG