Masu zanga-zangar dai sun hallara ne a harabar gidan gwamnatin jihar Neja dake Minna, domin nuna fushinsu kan matakin da gwamnatin jihar Neja ta dauka kan shugaban karamar hukumarsu.
Sai dai gwamnatin jihar Neja ta ce ana zargin shugaban karamar hukumar ne da sace kudi har Naira Miliyan 20 ta malaman makarantar fimare da suka yi ritaya, wanda hakan yasa aka dakatar da shi domin gudanar da bincike akai.
Shugaban tawagar matasan masu zanga-zanga, Mallam Abdulkadir Alfa, ya ce basu amince da dalilin da gwamnatin ta basu ba, suna mai neman a mayar musu da shugabansu kan kujerarsa.
Majalisar Dokokin jihar Neja ce ta bankado tabargazar da aka ce shugaban karamar hukumar ya aikata. Shugaban kwamitin labarai na Majalisar, Sha’aibu Liman Iya, yace an kama shugaban karamar hukumar ne da badakalar kudi kuma an bashi shawarar ya mayar da kudaden amma bai mayar da su ba.
Kwamishinan labarai na jihar Neja, Mr. Jonathan Batsa, ya ce gwamnatinsu ta APC ba zata ragawa duk wani da aka samu da laifin yin awon gaba da kudaden jama’a ba. ya kuma kira matasan da ke zanga-zanga da cewa hayarsu aka yi.
Domin karin bayani saurari rahotan Mustapha Nasiru Batsari.
Facebook Forum