An kaiga wannan matsayin ne bayan da shugaban ya mikawa Majalisar Dattawan Najeriya wasikar shaidawa majalisar cewa ya dawo kamar yadda kundun tsarin mulkin Najeriya ya tanada.
Yau shugaban ya hau kujerarsa kuma ya fara ganawa da manya manyan jami'an gwamnatin kasar da suka hada da mataimakin shugaban kasa Farfasa Yemi Osinbajo wanda ya ba shugaban bayanan abubuwan da suka gudana lokacin da baya kasar.
Sauran jami'an gwamnati dai dai da dai dai suna zuwa gaban shugaban suna yi masa bayanai akan ayyukansu, da abubuwan da suka faru da kuma irin matakan da suka dauka.
Malam Garba Shehu, kakakin shugaban ya yiwa Muryar Amurka karin haske dangane da yau ta kasance a fadar gwamnati. Yace basu san abubuwan da shugaban ya tattauna da mataimakinsa ba amma kuma saboda shugaban ya dade yana waje ba zai kama aikinsa da garaje ba. Wajibi ne ya san inda aka kai aka kuma tsaya.
Shugaban dai ya nuna godiyarsa ga 'yan Najeriya tare da kara jaddada dagewarsa wajen rike amanar 'yan kasar da nufin kyautata rayuwarsa.
Ga rahoton Umar Faruk Musa da karin bayani.
Facebook Forum