Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manoma Sun Yaba da Hana Shigo Da Shinkafar Kasashen Waje


Shinkafar da aka noma a Najeriya
Shinkafar da aka noma a Najeriya

Wasu jihohi tare da hadin gwuiwar manoman shinkafa a Najeriya sun yaba da matakin da gwamnatin Najeriya ta dauka na hana shigowa da shinkafa ta kan iyakokin kasar.

A cewarsu matakin ya taimaka wajen bunkasa noman shinkafa a kasar saboda ya zaburar da mutane da dama sun koma nomanta.

Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi daya daga cikin jihohin dake noman shinkafa yace matakin ya taimaka wajen samarda ayyukan yi ga dimbin manoma da matasa.

Yayinda yake jawabi wajen bada lambar yabo ga jihohi da manoman da suka yi suna wajen noman shinkafa da aka gudanar a birnin Legas, gwamnan ya bayyana matakin da cewa abun yabawa ne matuka.

Yana mai cewa shinkafa da ake shigowa da ita, shinkafa ce da ta dade a ajiye daga inda ake kawota saboda haka ba shinkafa ba ce da za'a kwatanta da ta Najeriya. To sai dai saboda masu saye basu san haka ba, suna sayenta suna tunanen sun samu arha alhali kuwa guba ce. Hukumar NAFDAC ta sha gwada shinkafar ta kuma tabbatar bai kamata ana cinta ba.

Abu na biye da shi inji Gwamna Bagudu shi ne wasu kasashe masu karfi suna karya farashin abincin da ake daukowa daga wurinsu domin su hana 'yan Najeriya noma nasu. Yace saboda haka sun ji dadin shirin gwamnatin tarayya tare da taimakon da ta bayar.

Jihar Legas tana hada gwuiwa da jihar Kebbi domin samun shinkafa da aka lakabawa suna Lek Rice.

Alhaji Aminu Goronyo shi ne shugaban kungiyar manoman shinkafa a Najeriya kuma yayi karin bayani dangane da alfanun da manoma shinkafan suka samu. Yace idan aka cigaba da tafiyar da suka soma to ko shakka babu zasu iya ciyar da kasar har su fitar da ita zuwa kasashen waje.

Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG