Karin kudin wutar lankarkin da ya kai kashi 45 a Najeriya na ci gaba da haddasa muhawara mai zafi, biyo bayan zanga zangar da ta kai ga Majalisar Dokoki, kungiyoyin kwadago sun kuduri aniyar kalubalantar wannan karin da zai jefa yawancin yan Najeriya cikin kunci a dai dai lokacin da farashin kayan masarufi ke kara karuwa saboda faduwar darajar Naira a kasuwar canji.
Sanata Kabiru Gaya, yace majalisar Dattawa zata dau mataki na tabbatar da janye wannan karin mai tsada, ya kara da cewa wannan karin bai dace ba saboda an sayarwa da kamfanin wuta cikin sauki, mai makon idan zasu kara kudi su kara da kaso 5 ko 10 amma suka kara har da kaso 45, daga karshe dai ya tabbatar da cewa Majalisa zata saka baki domin a gyara.
Majalisar Wakilai ma ta bi sahun Dattawan wajen adawa da wannan karin. Kamar yadda Ustaz Yunus Abubakar ke cewa tun lokacin da ‘yan Majalisar Wakilai suka ji kishin kishin labarin za a kara kudin wuta, suka riga sukayi wani kuduri da kuma zartar da shi, wanda yake cewa dole ne kamfanin ya dakatar da karin da zaiyi.
Sai dai Ministan Wuta Babatunde Fashola, ya bada hakurin kuncin da karin zai haifar, yana mai nuna hakan wani mataki ne na samar da wutar ba tare da yawan daukewa ba. A halin yanzu dai karfin wutar lantarkin Najeriya ta kai kusan Kilowat dubu biyar da ‘yan motsi.
Domin karin bayani.