Wani rahoto da ayarin wasu kwararru karkashin mai baiwa shugaban Najeriya shawara kan al’amuran da suka shafi makomar yan gudun hijira Dakta Meriam Masha da aka fitar a makwon jiya ya nuna cewa rikicin mayakan Boko Haram, a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, yayi sanadiyar asarar dukiya ta Dala Biliyan 9 baya ga salwanta asarar rayukan duban mutane cikin shekaru biyar da suka wuce.
Rahotan yace yanzu haka akwai kimanin mutane Miliyan 2 dake sansanonin yan Gudun Hijira dabam dabam bayan da maharan Boko Haram suka tarwatsasu. Kuma ana bukatar kimanin kudi Dala Biliyan 6 domin farfado da rayuwarsu cikin shekaru 4 masu zuwa, a fannonin kiwon lafiya da ilimi da aikin Noma da kuma sha’anin kasuwanci.
Tuni dai masana suka fara tsokaci kan wannan yunkuri, Aminu Buba Dibali, wanda ke zama manaja mai kula da shiyyar Arewa maso Yamma na shirin wanzar da zaman lafiya da sulhunta jama’a a Najeriya. yace ya kamata a zauna da shugabannin mutane da na kungiyoyi domin tantance abinda ya kamata ayi.
Saurari cikakken rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.