Ziyarar zata ba kasashen biyu damar fitowa da wasu matakan farfadowa da tattalin arzikin Najeriya daga bangaren cinikayya da wutar lantarki da kuma sha'anin noma.
Tuni tawagar shugaba Buhari ta share fagge ta kama hanyar zuwa China.
Kakakin shugaban Najeriya Malam Garba Shehu ya kara bayani akan mahimmancin ziyarar.
Shugaba Buhari zai je China ya tattauna da shugaban kasar Xi Jinping akan mahimman abubuwa. Akwai abubuwan da kasar China take sha'awa a Najeriya. Akwai maganar layin dogo wanda an dade ana maganarsa. Ana son a yi sabo tsakanin Legas zuwa Kano da ma wasu wuraren. Akwai kuma maganar wutar lantarki. Idan tattaunawar ta tafi daidai kasar China zata shiga Najeriya da kudaden da za'a yi ayyukan dasu.
To saidai kudin da China zata tanada ba tallafi ba ne . Bashi ne. Amma ayyukan su ne zasu biya bashin.
Ga karin bayani