Daliban sun rufe harabar jami'ar ba shiga ba fita yayinda suke zanga zangar tare da kin magana da 'yan jarida.
Kamar yadda wasu shugabannin daliban suka shaidawa wakilin Muryar Amurka a kebe sun ce akwai niyar dokacin jami'o'in tarayyar Najeriya su bi sahun na Legas su gudanar da zanga-zanga dangane da halin da Najeriya ta samu kanta ciki.
Zanga-zangar daliban na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar kwadago ta kasa tace zata gudanar da wani yajin aiki na gargadi domin jawo hankalin gwamnati akan tsananin karancin man fetur da na wutar lantarki da kasar ke fuskanta.
Shugaban kungiyar kwadago ta kasa Ayuba Waba yace sanin kowa ne da akwai wasu suna biyan kudin lantarki nera dubu biyu amma yanzu nera dubu goma sha biyu suke biya duk da cewa babu wutar. Yace saboda haka zasu gudanar da wani yajin aiki na gargadi domin hukumomi su kawo karshen wannan matsala.
Duk da zanga zangar daliban da barazanar zuwa yajin aiki da kungiyar kwadago keyi wasu 'yan Najeriya suna nuna goyon bayansu ga shugaba Buhari suna kiran jama'ar kasar da su yi hakuri da Shugaba Buhari. Sun ce cin hanci da rashawa sun yiwa kasar katutu kuma za'a dauki lokaci kafin a shawo kan matsalar. Da sannu a hankali Buhari zai ciwo kan matsalolin.
Ga karin bayani.