Madam Gloria Laraba ta ce sun yi murna kwarai da aka samo 'yan matan makarantar Jange6e. Koda yake ta ce akwai dalibai maza da ake sace kamar na Kankara 300 da kuma na Kagara 27 amma mata sun fi yawa musamman a makarantun mata ta shiyyar Arewa.
Laraba Shoda ta yi misali da 'yan mata 276 a Chibok da 105 da aka sace a Dapchi ta Jihar Yobe sai kuma 279 da aka sako yanzu a Jange6e ta Jihar Zamfara. Ta kara da cewa matsalar ta fi kamari a Arewa inda karatun 'ya'ya mata ke da muhimmanci.
Amma tsohuwar Shugabar Mata ta Jamiyyar CPC Hajiya Hafsatu Aliyu ta yi korafi cewa an fi samun koma baya a ilimin mata a Arewa, amma tana ganin ya kamata a rufe dukkan makarantun kwana na mata indai Gwamnati ba za ta iya tsare su ba.
Hafsatu Aliyu ta ce gara su rika fita daga gida suna zuwa karatun idan haka zai sa a yi karatun a cikin kwanciyar hankali.
Amma kuma Shugabar Kungiyar Mata da Yara ta Az-Zawaj Hajiya Asma'u Abe Wala ta yi tsokaci cewa bai kamata a hana 'ya'ya mata zuwa makaranta a Arewa ba, saboda dama Arewa ita ce koma baya a ilimi musamman ma na 'ya'ya mata.
Asma'u Abe Wala ta ce da biyu ake yi don a karya ilimi a Arewa din musamman ma na 'ya'ya mata, saboda haka tana ganin gara mahukunta su yi nazari sosai wajen kawo mafita a harkar tsaron makarantun, inda ta ce a rika gina wuri na musamman domin jami'an tsaro a dukkan makarantu, kuma a tabbatar cewa suna da kayan aiki sosai.
Abin jira a gani shi ne irin matakin da Gwamnati za ta dauka wajen tabbatar da tsaro a makarantun Gwamnati, ko na mata ko na maza domin yara manyan gobe su samu ilimi da zai amfane su nan gaba, saboda a gudu tare a tsira tare.
A sauti rahoto cikin sauti daga Medina Dauda: