Sakamakon munanan hare-haren ta’addancin da suka kakkai a cikin kasar ta Faransa. Duk da yake ba dukkan Masallatan kasar kimanin 2,500 ne ke cikin wannan tsarin wayar da kan ba.
Amma fitattun masallatai na ciki, kamar babban masallacin dake babban birnin kasar da aka fi sanin da Grand Mosque of Paris. Shugaban hadakar al’ummar Musulmin Anouar Kbibech ya yiwa manema labarai bayani.
Inda yace Masallatai na gayyatar al’umma da ba musulmi ba da su je masallatan su halarci lafiyayya tare da Musulmai don a zagaya da su cikin masallatan tare da ci da sha, a kuma yi musu bayanin yadda addinin musulunci yake.
Hakan zai hada da tarurrukan wayar da kai a cikin masallatan da ma basu damar ganin yadda Musulman ke yin daya daga cikin sallolinsu biyar a rana. Duk wannan abu da nufin nunawa duniya cewa Musulunci addinin zaman lafiya ne ba yadda 'yan ta'adda ke bata sunan mabiyansa ba.