Kotun koli ta Jamhuriyar Nijar, ko kotun tsarin mulki, ta tantance mutanen da ta ce sune suka dace su tsaya takarar kujerar shugabancin kasar a babban zaben da za a gudanar a ranar 21 ga wata mai zuwa na Fabrairu.
A bayan da ta shafe tsawon mako guda tana nazarin takardun mutane 16 wadanda ma'aikatar harkokin cikin gidan Nijhar ta mika mata a matsayin wadanda suka nuna sha'awar tsayawa takara, kotun ta amince da takardun mutane 15, yayin da ta yi watsi da na wani mutum guda a zaman wanda bai cika ka'idar tsayawa takarar ba.
Sanarwar kotun ta ce Abdoulkarim Bakasso na jam'iyyar PDP-Annour, bai gabatar da cikakkun takardun da suka kamata na tsayawa takarar shugabancin kasar ba, a saboda haka ta yi watsi da aniyarsa ta neman tsayawar.
Hukumcin wannan kotu dai shine na karshe.
'Yan takara guda 15 da kotun ta amince su shiga zaben na shugaban kasa sune:
1-Tahirou Guimba (MODDEL MA AÏKATA)
2-Amadou Djibo dit Max (UNI)
3-Mai Moussa Lawan Gaptia (Indépendant, UNION DES INDEPENDANTS ASKER)
4-Mahamane Jean Padonou (CDP MARHABA)
5- Abdou Labo (CDS RAHAMA)
6-Hama Amadou (MODEN LUMANA)
7-Seyni Oumarou (MNSD NASSARA)
8-Issoufou Mahamadou (PNDS TARRAYA) - Shugaba Mai Ci
9-Mahamane Ousmane (MNRD HANKOURI)
10-Ibrahim Yacouba (MPN KICHIN KASSA)
11- Amadou Boubacar Cissé (UDR TABBAT)
12-Moctar Kassoum (CPR INGANCI)
13-Cheiffou Amadou (RSD GASKIYA)
14-Mahamane Hamissou (PJD HAKIKA)
15-Abdoulaye Traoré (PPNU)