Zanga zangar kin jinin gwamnati ta ratsa babban birnin kasar da kuma kudancin kasar wanda ‘yan Shia’a suke da rinjaye tun a watan Oktoba, inda mutane suke zanga zanga akan cin hanci da rashawa, rashin ababen more rayuwa da rashin aikin yi.
Shugaba Barhama Salih da ‘yan majalisa sun kasa cimma matsaya a wa’adi da dama da aka basu don su sanar da sabon firai Minista, biyo bayan ajiye aiki da Adel Abdul Mahdi ya yi a watan da ya gabata. Mahdi da gwamantin sa sun amince za su ci gaba da zama a matsayin gwamnatin rikon kwarya har sai an amince da sabon Firai Minista.
Ajiye aikin da Mahdi ya yi har yanzu bai gamsar da masu zanga zangar kin jinin gwamnati ba wadanda suka ce wannan bai wadatar ba a samu wani sabon Firai Minista ya ja ragamar kasar. Suna neman a samu canje canje gaba daya a tsarin siyasar kasar da aka kakaba musu bayan da Amurka ta mamaye kasar a shekarar 2003, wanda suka ce yana cike da cin hanci, kana bai magance komai ba wajan taimakawa Iraqi duk da irin arzikin man da kasar take da shi.
Facebook Forum