To amma a cewar shugaban hadaddiyar kungiyar matasan arewa Imrana Wada Nas da sauran rina a kaba.
Yace ya kamata shugaba Buhari ya kawo agenda ta mutanen arewa domin wai, har yanzu agendar da shugaba Buhari yake karantawa bata mutanen arewa ba ce. Yace babbar agenda da suka sa gaba ita ce ta jawo ruwan teku daga kudu zuwa kogin kwara da ya hadu da na binuwai a Lokoja. Idan aka yi hakan maimakon mutanen Kano, Sokoto, Katsina ko Zamfara su dinga zuwa Legas dauko kaya sai su dauka a Lokoja. Kana dubban mutane zasu samu aikin yi.
Imrana ya cigaba da cewa irin wuraren da aka gano suna da mai a tabbatar cewa daga nan zuwa badi ana kokarin hako man a arewa. Saidai wai duk wadannan har yanzu Buhari bai sasu a tunanensa ba.
Hajiya Yalwan Shata tace abubuwa hudu da shugaba Buhari ya sa a gabansa zai yi abubuwa ne dake da wuya. Amma babban abun da yakamata ya mayarda hankali kai shi ne yadda zai kubutar da talaka daga cikin wahalar da ya samu kansa tun daga lokacin da Buhari ya hau mulki. Dalili kuwa shi ne karancin abinci da yanzu ya yiwa kasar katutu.Kafin Buhari ya hau mulki buhun shinkafa dubu takwas ne amma yanzu ana sayar da shi dubu goma sha bakwai ko sha takwas. Ta bada shawarar a bude iyakokin kasa a bar mutane da suka sayo shinkafa su shigo da ita su biya kwastan. Idan ta wadata gwamnati na iya sake rufe iyakokin.
Amma Tijjani Kyari Muhammad daya daga cikin matasan jam'iyyar APC yace Buhari yayi rawar gani. Maganar tashin bamabamai ta yi sauki. Saidai ya kira wadanda suke tare da shi su dinga bashi shawara da hadin kai.
Ga karin bayani.