Shugaba Buhari yace ya amince da daidaita tafiyar da manufofin ka'idodin kudi da kuma yadda ake kashe kudin a shekara.
Shugaban yace zasu zuba ido domin ganin sabbin matakan da suka dauka kwananan ko zasu yi tasiri kan darajar nerar da tattalin arzikin Najeriya. Yace a sani cewa kudi masu daraja nada rawar da suke takawa ga karfin tattalin arzikin kasa.
Wannan bayani na shugaban karin haske ne kan matakin da babban bankin kasar ya dauka na barin nera ta samar ma kanta farashi a kasuwa. Saidai nan take farashin dala ya tashi zuwa nera 350 kan kowace dala lamarin da ya sa farashin kayan masarufi ma suka haura sama har da ma kayan da basu da alaka da dala.
Shugaban kungiyar ma'aikatan kananan hukumomin Najeriya Kwamred Ibrahim Khalil ya nuna damuwa da cewa ta'allaka farashin man fetur kan dala ko sa dalilan man fetur su samar ma kansu dala zai yi tasiri wajen kara tayar da farashin kayan masarufi.
Khalil yace duk lokacin da aka kara farashin man fetur to ko farashinsa a kasuwar bayan fage dada karuwa yake yi. Yace babu dan kasuwar man fetur da zai sayi dala da tsada ya sayo mai kana a ce ya sayar dashi akan farashin da ba zai fita ba.
To amma gwamnati a nata bangaren na jin matakan samun kudade ne da zata aiwatar da kasafinta na kudi da ya kai sama da nera tiriliyon shida saboda hakan ne zai sa ta cika alkawuran kemfen da tayi.
Ga karin bayani.