Yayin da shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya, ke cika shekara daya bisa gadon mulki, ‘yan Najeriya, na cigaba da bayyana ra’ayoyin su. Yayin da wasu ke yabawa, wasu kuma na cewa akwai bukatar sassauci musamman a bangaren matakan yaki da barna.
Abin da ‘yan Najeriya, su ka fi yin ittifaki akai shi ne, cewa gwamnatin ta Buhari ta yi nasarar kassara kungiyar 'yan ta'adda ta Boko Haram, inbanda abin da ba a rasa ba. Wani dan babbar jam’iyyar adawa ta PDP mai suna Lamido Umar Chekere, ya gaya ma wakilin mu a Abuja, Saleh Shehu Ashaka, cewa Buhari ya yi amfani da sanayyarsa ta aikin soja, wajen tarwatsa ‘yan Boko Haram.
Haka zalika, tsohon Minista Ido Hong, ya gaya ma Ashaka, cewa Najeriya, ta doshi Alkibla madaciya musamman, dangane da tsaro da kuma yaki da cin hanci da rashawa. Amma ya ce dole ‘yan Najeriya, su yi hakuri saboda barnar da Buhari ke gyarawa ta na da yawan gaske.
Shi kuma wani dan canjin kudi mai suna Jibrin Zaka, ya ce shi fa bai gani a kar ba. Ya ce batun satar da ake zargin jam’iyyar PDP da tafkawa ma, ya kula cewa kowani gauta ja ne. Dalilinsa kuwa shi ne, da yawa daga cikin kujerun da APC ta ci, tsoffin kurayen PDP ne su ka sake dawowa, kai da sunan APC.
Shi kuwa wani dattijo mai suna Alhaji Musa Yola, ya ce wasu ‘yan Najeriya sun cika gaggawa da rashin hakuri, da kuma rashin danganta laifi ga inda ya dace. Ya kara da cewa matsalar da ake fama da ita yanzu ta fi alaka da rashin noma abinci sosai bara saboda dalilai daban-daban. Ya na mai kira ga ‘yan Najeriya, da su dai-dai ta rayuwar su ta dace da halin tsimin da ake ciki.