Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masana Sun Gargadi ECOWAS Dangane Da Daukar Matakan Soji A Nijar


Taron kungiyar ECOWAS a Abuja
Taron kungiyar ECOWAS a Abuja

Bayan taron ECOWAS a babban birnin Abuja, inda shugabanin suka amince da fara aiki da rundunar da ke shirin shiga tsakani a Nijar duk da cewa, tana son a maido da mulkin dimokradiya cikin lumana, kwararru a fanin zamantakewan dan Adam da 'yan siyasa sun ja hankali shugabanin kan daukan matakan.

Shugabanin Kasashen Afirka ta Yamma sun ce duk wani zabi da zai sa su hada da amfani da karfi ya rage kan teburin maido da tsarin mulki a Nijar bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Yuli tare da ba da umurnin fara aiki da rundunar ta.

Kungiyar ta yi alkawarin aiwatar da takunkumi da hana tafiye- tafiye kan wadanda ke hana sake dawowa da hambararren shugaba Mohammed Bazoum kan karagar mulki. Kungiyar ta kuma ce anfani da karfi shi ne mafita ta karshe.

A hirar shi da Muryar Amurka, Dokta Farouk Bibi Farouk Kwararre a harkar siyasar kasa da kasa kuma malami a jami'ar Abuja, ya ce matakan da kungiyar ta dauka kwanaki 10 da suka wuce har yanzu a kan matakan ake. Bibi ya ce idan an bincika Kungiyar ECOWAS ba ta da wasu sojoji a ajiye da za su iya yi masu wannan aiki da kungiyar ta ke tunani, domin yanzu babu ECOMOG a kasa.

Bibi ya ce babu kasar da za ta iya daukan sojoji 10,000 zuwa ko ina, Najeriya ce kadai za ta iya daukan wannan mataki, ita din ma a matse za ta iya diban sojoji 10,000 kuma wannan zai iya zama babbar magana, saboda haka sai an samu sojoji da za a yi amfani da su, a kawo gudumawa daga wani waje. Bibi ya ce kasa kamar Nijar da ta ke da girma da fadi da yawan mutane kusan miliyan 27, zai yi wahala a zo daga waje a canza masu abinda suka dauka suna yi. Ko da an samu adawa da matsayin sojojin nan da suka dauka, za su yi nesa da babban birnin kasar.

Haka kuma, Shugaban Kungiyar Sanatocin Arewa a Majalisar Dattawa, Abdul Ningi ya ce babu inda kundin tsarin mulki ya ba shugaban kasa hurumi na daukan irin wannan mataki sai Majalisar kasa ta bashi dama.

To sai dai ga daya cikin masu bibiya da nazari kan harkokin kasashen waje Ali M. Ali ya yi tsokaci cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu baya daukan mataki a matsayin sa na Shugaban Kasar Najeriya, Sai dai a fahimci cewa yana aiki ne da wadannan kasashe 15 a matsayin sa na shugaban kungiyar. Ali ya ce ba lailai ba ne a far ma Nijar tunda ba zai yiwu ba sai an samu amincewar Majalisar kasa har idan ta kama ma a samu amincewar sauran kasashen ba ki daya.

Duk da wadannan matakai da kungiyar ECOWAS ta dauka bai hana jagororin juyin mulkin Nijar nada sabuwar gwamnatin wucin gadi ba domin Mahamane Roufai Kaouali wanda aka ambata a matsayin Sakataren Gwamnati ya nada ministoci 21 ba tare da bayyana wasu shirye shiryen gwamnati ba.

Saurari rahoton a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:53 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG