Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Marwa Na So A Rika Yi wa Daliban Jami’a Gwajin Amfani Da Miyagun Kwayoyi


Shugaban NDLEA, Muhammad Buba Marwa (Twitter/ NDLEA)
Shugaban NDLEA, Muhammad Buba Marwa (Twitter/ NDLEA)

Shugaban hukumar da ke yaki da amfani da miyagun kwayoyi ta NDLEA, Janar Buba Marwa mai ritaya, ya yi kira da a samar da wani tsari da za a rika yi wa daliban jami’a da sauran manyan makarantu gwajin da zai tantance ko suna tu’ammuli da miyagun kwayoyi ko akasin hakan.

Hukumar ta NDLEA ta ce akwai bukatar a samar da wannan tsari ba a jami’o’i kadai ba, har ma da sauran manyan makarantun gaba da sakandare.

Marwa ya yi kiran ne yayin kaddamar da wani shirin yaki da amfani da miyagun kwayoyi a Jami’ar Abuja a ranar Laraba.

Shugaban na NDLEA ya ce akwai bukatar a hada kai tsakanin hukumar da jami’o’in Najeriya ta yadda za a kafa ofisoshi a cikin makarantun don karfafa yaki da wannan mummunar dabi’a

Tsarin na gwajin zai hada da tsoffi da sabbin dalibai da za a diba a makarantun a cewar shugaban hukumar ta NDLEA.

Marwa ya kara da cewa, matsalar amfani da miyagun kwayoyi ta zama babban abin damuwa a Najeriya musamman a tsakanin matasa.

Shugaba Donald Trump ya ba gwamnatinsa damar tasa keyar bakin haure daga kasar, da kai wasu kurkuku na Guantanamo Bay dake Cuba
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Shehu Kanam mai sharhi kan al’amura ya mana karin bayanin matsayin dalilan yawaitar fashewar tankokin man fetur a Najeriya
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:23 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Karin haske akan dalilan dake kawo aukuwar haduran tankar mai a Najeriya da musabbabin karuwar wannan lamari a baya-bayan nan
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:37 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG