Hukumar NDLEA da ke yaki da masu sha da safarar miyagun kwayoyi a Najeriya ta ce ta kama kwayoyin Tramadol kusan miliyan 1.5 yayin da aka nufi garin Yauri a jihar Kebbi da su.
Cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi dauke da sa hannun Darektan yada labaranta, Femi Babafemi, hukumar ta NDLEA ta ce an dauko kwayoyin ne daga birnin Onitsha da ke jihar Anambra a kudu maso gabashin kasar.
Jami’an NDLEA ne suka kama motar da ke dauke da kwayoyin yayin da ta ratsa ta jihar Edo don danganawa da Kebbi.
“Kwakkwaran binvike da aka gudanar akan motar ya sa aka gano kwayoyin wadanda aka boye su a karkashin wasu wasu kayayyaki.”
“Mun yi nasarar kama wadannan kayayyaki ne bayan bayanan sirri da muka samu.” In ji Babafemi.
Kazalika hukumar ta ce a ranar da aka kama kwayoyin an Tramadol da aka nufi Kebbi da su, ta kuma kama kwayoyin Diazepam 425,000 a Segemu, Kano.
A wani labari na daban, hukumar ta NDLEA ta ce ta kama miyagun kwayoyi da nauyinsu ya kai kilo 137, 754 a hannun wani “kasurgumin” dan fashin daji mai safarar miyagun kwayoyi a jihar Filato.
Cikin sanarwar, Babafemi ya ce sun kuma karbe Naira miliyan 1.4 da harsashai daga hannun dan fashin dajin.