Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya (NDLEA), ta kama wani mutum da ake zargin kasurgumin dillalin miyagun kwayoyi ne mai suna Okey Eze, a filin sauka da tashin jirage na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja babban birnin kasar.
An kama Eze ne dauke da nadi 350 na hodar Iblis wanda kudin sa ya kai Naira biliyan biyu da digo uku (N2.3bn)
Eze mai shekaru 38 dan asalin karamar hukumar Oji-River a jihar Enugu, ya shiga hannun jami'an hukumar ne a ranar Laraba, a yayin da ake tantance fasinjoji kafin shiga jirgin saman Ethiopian airline zuwa birnin Addis Ababa.
Miyagun kwayoyin wadanda nauyinsu ya kai nauyin Kilograms 7.7, an nade su ne a cikin fakiti guda takwas, inda ya sanya su a wurare mabanbanta a cikin kayayyakin da zai yi tafiya da su.
A yayin da yake bayani, Eze, wanda yake mazaunin garin Bamako ne na kasar Mali, ya ce ya bi ta hanyar gabar Seme Badagry, a jihar Legas tun a shekarar 2019.
Ya kuma bayyana cewa yazo Najeriya da kwayoyin saboda ya sami kudaden shiga da zai kula da yaran dan uwan sa da ya rasu guda hudu.
Kazalika mutumin yayi ikirarin cewa abokin sa mazaunin kasar Brazil ne ya umurce shi da ya dauki wannan jakar da ke dauke da kwayoyin, bayan da ya nemi abokin ya taimake shi da kudi.
Eze ya ce ya dauko jakar ya hauro jirgi da ita daga Addis Ababa zuwa Najeriya, inda zai baiwa wani wanda za'a aiko masa da adireshin sa idan ya iso.
A nashi bangaren Shugaban hukumar NDLEA, Burgediya Janar Mohamed Buba Marwa mai ritaya, ya jinjinawa jami'an hukumar reshen NAIA wadanda suka yi nasarar cafke Eze, ya kuma ce hukumar za ta ci gaba da yaki da masu yunkurin mayar da Najeriya matattarar ajiye miyagun kwayoyi.