ABUJA, NIGERIA - Sakamakon yakin dake tsakanin kasar Rasha da Ukraine da ya haddasa koma baya a bangarori da dama a duniya, da suka hada da hauhawar farashin kayayyaki, masana a Najeriya na cewa idan har kasar bata canza tsarinta na sayen takin zamani daga kasashen Rasha da Ukraine ba, to ba shakka matsalolin karancin taki da hauhawar farashin kayaki zai kara tsananta.
Kwararre kan harkar noma a Najeriya, Yunusa Ishiaku, ya fadi cewa takin da gwamnati ke sayar wa manoma a da cikin farashi mai rahusa ya samu kutse daga masu gurbata shi, abinda ke rage amfanin noma da ake bukata.
Sakamakon yakin dake tsakanin kasar Rasha da Ukraine da matsalar tsaro da Najeriya ke fama da ita, ga batun matsalar tsadar man fetur da na dizal, masana na ganin idan aka yi sakaci wajen daukar matakan samar da taki na gargajiya, ba shakka kasar za ta shiga mawuyacin hali, a cewar masani kan tattalin arzikin kasa, Nasiru Marmara.
Ministan ayyukan noma da raya karkara a Najeriya, Dakta Muhammad Mahmud Abubakar, ya ce gwamnati na iya kokarinta wajen tunkarar matsalar.
Cikin wani rahoto da hukumar abinci da fannin ayyukan noma ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar, an yi gargadin cewa ‘yan Najeriya miliyan 19 da dubu dari hudu na iya fuskantar matsanancin karancin abinci a tsakanin watan Yuni da Agustan wannan shekara ta 2022.
Kuma an kiyasta cewa farashin kayayyakin abinci zai karu a yankin Saharar Afirka da kaso 30 zuwa 40 cikin dari akan sauran yankunan duniya.
Saurari rahoton daga Shamsiyya Hamza Ibrahim: