Kungiyar manoman shinkafa a kasar tare da hadin gwiwar kamfanin Syngenta dake samar da magunguna da iri na noma sun bayyana hanyoyin da manoma musamman na shinkafa za su bi wajen inganta amfanin nomarsu don tabbatar da an samar da wadataccen abinci a kasar.
A ci gaba da kokarin ganin an samar da wadataccen abinci a Najeriya, masana daga ciki da wajen kasar tare da hadin gwiwar kungiyar manoman shinkafa ta Najeriya wato RIFAN sun gudanar da wata bita na karawa juna sani game da yadda za’a samu Karin albarkatun noman shinkafa da kuma hanyoyin da za’a magance matsalolin dake hana samun amfanin gona mai yalwa a kasar
La’akari da kalubale na hauhawar farashin kayayyakin abinci a Najeriya da ma matsalar karancin abincin da wasu kasashen duniya ke fuskankanta sakamakon yakin da ke tsakanin kasar Rasha da Ukraine ya haifar.
Kungiyar manoman shinkafa a kasar tare da hadin gwiwar kamfanin Syngenta dake samar da magunguna da iri na noma sun bayyana hanyoyin da manoma musamman na shinkafa za su bi wajen inganta amfanin nomarsu don tabbatar da an samar da wadataccen abinci a kasar da kuma kaiwa wasu kasashen ta sabin hanyoyin yaki da ciyawa dake janyo barazana wajen samun yalwa a abin da aka noma.
A duk shekara dai kusan tan miliyan 7 na shinkafa ake ci a Najeriya kuma kama daga noman ta ya zuwa taki da da ma sarrafa shinkafar dai, sama da mutane miliyan 12 ne ke samun aiki daga albarkar noman hekta dubu dari biyar na shinkafar a shekara, baya ga dubban miliyoyin Naira da ke shiga aljihun manoma da masu sarrafa shinkafa a kasar.
Hakan ya sa kungiyoyin biyu, suka hada Manoma daga jihohi 36 har da babban birinin tarayyar Najeriya Abuja don cin moriyar sabin hanyoyin inganta amfanin nomarsu na shinkafa.
Hamza Ahmad Mahuta shine babban jami’in bada shawarwari ne na kamfanin Syngenta.
Daya daga cikin manoman da suka samu halartar taron Aisha Mohammad Bature ta bayyana cewa taron ya zo a kan lokacin da ake bukatarsa duba da yanayin hauhawar farashin kayyakin abinci a kasar.
Tuni dai Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci shugabannin kasashen duniya da su hada kai wajen tsara hanyoyin dakile matsalar karancin abinci da ta kunno kai a duniya wanda ya kara kamari musamman a nahiyar Afrika sakamakon yakin Ukraine da Rasha.
Saurari cikakken bayani daga Shamsiyya Hamza Ibrahim: