Malaysia ta mika takardar kuka a hukumance ga jakadan Singapore dake Kuala Lumpur, kan kalamai marasa dadi da kungiyar WikiLeaks ta bayyana,cikin takardun sirrin Amurka.
Yau Talata,ma’aikatar harkokin wajen Malaysia ta fidda sanarwa inda ta bayyana “matukar rashin jin dadinta” kan kalaman, cikin takardar da ta mikawa jakadan Singapore. Ranar lahadi, wata jaridar Australia, ta buga bayanan sirrin difilomasiyyar Amurka, da ya nuna jami’an Singapore suna radar kasashe makwabta da batunci. Kasashen sun hada da Malaysia,Thailand,India,da kuma Japan.
An ambaci jami’an suna zargin “Yan siyasa da basu da kan gado” a Malaysia, da janyo wani “yanayi na rudani mai hadari” cikin kasar. Suna gargadin sai tayu Malaysia ta fuskanci fitinar kabilanci,da zai iya sanya ‘yan kasar China dake Malaysia, su shiga gudun hijira zuwa Singapore.
Jiya litinin, jami’an Singapore suka bayyana kwarin guiwar cewa dantakarsu da makwabtanta yana da karfin hana fallasar yi musu illa.