Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tattaunawar Zaman Lafiya a Gabas ta Tsakiya Na Fuskantar Barazana


Jakadan Amurka Tattaunawar Zaman Lafiyar Gabas ta Tsakiya George Mitchell ( a dama) da Shugaban Falasdinwa Mahmoud Abbas birnin Ramallah na Yamma da Kogin Jordan a ran 14 Dis. 2010
Jakadan Amurka Tattaunawar Zaman Lafiyar Gabas ta Tsakiya George Mitchell ( a dama) da Shugaban Falasdinwa Mahmoud Abbas birnin Ramallah na Yamma da Kogin Jordan a ran 14 Dis. 2010

Fatan cimma maslaha tsakanin Isira’ila da Falasdinawa zai fara dusashewa a badi, mutukar dai ba a sami wani cigaba a yinkurin sasantawar da Amurka ke yi ba.

Jakadan Majalisar Dinkin Duniya Na Musamman a Gabas Ta Tsakiya, ya ce fatan cimma masalaha tsakanin Isira’ila da Falasdinawa zai fara dusashewa a badi, mutukar dai ba a sami wani cigaba a yinkurin sasantawar da Amurka ke yi ba.

Robert Serry ya gaya wa Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya jiya Talata cewa ya na matukar muhimmanci a cimma yarjajjeniyar zaman lafiya a shekara ta 2011. Ya yi kira da a shigar da masu sasantawa tsundum cikin wannan tattaunawar ciki har da kasar Amurka, da Tarayyar Turai, da Majalisar Dinkin Duniya da kuma Rasha.

Jakadan Majalisar Dinkin Duniya na Musamman a tattaunawar zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya ya ce jami’ai daga hukumomin nan hudu za su gana a farkon 2011. Ya ce mutuncin masu daukar dauyin tattaunawar zaman lafiya da na ita kanta tattaunawar na fuskantar barazana.

Serry ya bayyana kin sake jinkirta gine-gine a matsugunan Yahudawa da Isira’ila ta yi da cewa babban koma-baya ne y ace ayanzu Amurka na shirin ta shawo kan Isira’ila da Falasdinawa su koma kan tafarkin tattaunawa a fakaice kan dukkannin batutun da yakamata a yanke shawara a kansu.

XS
SM
MD
LG