Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Holbrooke Ya Rasu


Marigayi Richard Holbrooke
Marigayi Richard Holbrooke

Gogaggen jami’in diflomasiyar Amurka, kuma manzon Amurka na musamman a kasashen Afghanistan da Pakistan, Richard Holbrooke, ya mutu a jiya litinin ya na da shekaru 69 a duniya.

Gogaggen jami’in diflomasiyar Amurka, kuma manzon Amurka na musamman a kasashen Afghanistan da Pakistan, Richard Holbrooke, ya mutu a jiya litinin ya na da shekaru 69 a duniya.

Ranar Jumma’a Holbrooke ya kamu da rashin lafiya ya na tsakar tattaunawa da sakatariyar harakokin wajen Amurka, Hillary Clinton. An gaggauta kai shi wani babban asibitin birnin Washington D.C, inda akai mi shi tiyatar awowi ishirin don a gyara wata tsaga a babbar jijiyar da jini ke bi daga zuciya zuwa sauran jiki.

Bayan wannan kuma a jiya lahadi an yi mi shi wata tiyatar.

Shugaba Barack Obama ya gabatar da wata sanarwa da yammacin jiya litinin, inda yake cewa ya na cikin matukar bakin ciki saboda mutuwar Holbrooke. Ya bayyana cewa gogaggen jami’in diflomasiyar toron giwa ne a huldar Amurka da kasashen waje, wanda ya taka rawar kara karfafa kasar shi da kara kiyaye ta da kuma kara daukaka ta.

Sakatariyar harakokin wajen Amurka Hillary Clinton ta ce, Holbrooke na daya daga cikin gagara gasar Amurka mafiya kwazo kuma daya daga cikin ma’aikatan gwamnati mafiya bautawa kasa.

Clinton ta fada cewa, ta samu sakonnin karfafa guiwa daga ko’ina a duniya saboda mutuwar gogaggen jami’in diflomasiyar wanda ya yi kusan shekaru hamsin a rayuwar shi ya na bautawa kasar Amurka.

Daga cikin manya-manyan abubuwan da Holbrooke ya yi a rayuwar shi, akwai muhimmiyar rawar da ya taka wajen kulla yarjejeniyoyin sulhu na Daytona wadanda su ka samar da zaman lafiya a Bosnia-Herzegovina. Yarjejeniyoyin da shugabannin Sabiya da na Bosniya da na Kroweshiya su ka rattabawa hannu a ranar hudu ga watan disemban shekarar 1995, su ne su ka kawo karshen munmunan yakin kabilancin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane dubu dari.

XS
SM
MD
LG