Hukumomi masu kula da magani na tarayyar kasashen turai, sun fada a yau Juma’a cewa za’a iya amincewa da a yi amfani da maganin mai suna Mosquirix ga yara da jarirai, duk da cewa ya nuna bambancin sakamako lokacin da aka gwada shi.
Kamfanin GlaxoSmithKline ne yayi maganin, tare da hadin gwuiwar gidauniyar Bill and Melinda Gates Foundation, wanda ya zamanto maganin su na Malariya na farko. A cewar hukumar lafiya ta duniya maganin zai taimaka wajen kare cutar cizon sauro da take kashe mutane dubu 584 duk shekara. Hukumar kula da lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya tace sama da kaso 75 cikin dari na mutanen da cutar Malariya ta kashe, yara ne kanana, kuma yawancinsu daga nahiyar Afirka suke.
A lokacin da ake gwada maganin an yi amfani da yara kanana ‘yan watanni 17 da haihuwa, an kuma ga cewar kashi 50 cikinsu maganin yayi musu aiki a shekarar farko.