Kimanin kashi ashirin da biyar a cikin dari na yawan yaran da ake Haifa a Najeriya ne ke mutuwa sanadiyar cututtuka dake da dangantaka da iyaye mata, da kuma cutar maleria.
Ministan kiwon lafiya na Najeriya, Dr, Haliru Alhassan ne ya bayan haka ga wakilin mu, a birnin Washington bayan da ya halarci taron akan kiwon lafiya inda kimanin kasashe ashirin da biyar daga Afirka da Asiya suka halarta.
Dr. Haliru Alhassan, yace alkaluma na nuni da cewa cutar malaria na kan gaba wajen sanadiyar mace-macen yara kanana da iyaye mata.
Yayi amfani da wannan damar waje kira ga jama’a dasu tsaftacen muhallinsu domin sauro samun wajen zama.