Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tinubu Zai Yi Takarar Tazarce a Zaben 2027 - Ganduje


Tinubu, Ganduje da Kwankwaso
Tinubu, Ganduje da Kwankwaso

A jiya Talata ne Ganduje yayi wannan furuci a sakatriyar jam’iyyar APC ta kasa a Abuja, a sa’adda ya karbi bakoncin mambobin kungiyar matasan Arewa masu goyon bayan Tinubu

Shugaban jam’iyar APC ta kasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa shugaba Bola Ahmad Tinubu zai yi takarar neman tazarce a 2027.

Ganduje yayi wannan furucin ne, jiya Talata a sakatriyar ofishin jam’iyyar APC a Abuja, a sa’adda ya karbi bakoncin mambobin kungiyar matasan Arewa masu goyon bayan Tinubu, sannan ya kara da cewa, Tinubu za iyi nasara a karo na biyu kuma zai yi mulkin Najeriya har zuwa 2031, lokacin da mulki zai dawo arewa bayan wa’adin shi na 2.

Jaridun Najeriya sun ruwaito cewa Dr. Danduje y ace “Muna farin cikin cewa jam’iyyar mu ta yadda da tsarin karba karba. Lokacin da dan Arewa karkashin jam’iyyar mu yake shugabancin kasar, mun tallata cewa shugaban kasa na gaba zai kasance daga kudancin Najeriya kuma cikin hukuncin Allah, mun yi aiki tukuru da taimakon ‘yan Najeriya dan kudu yayi nasara.

Ganduje wanda yayi gwamna a Jahar Kano da ke yankin arewa maso yammacin Najeriya mai yawan al’umma, ya ce jam’iyyar su za ta ba da goyon baya ga kungiyar don al’umma su amince da Tinubu gabanin babban zaben kasar da za ayi a shekarar 2027.

Ya kuma karbi bakoncin wata kungiya mai goyon bayan Tinubu kuma, wanda ake kira da “Young Generation Forum, a sakatriyar jam’iyyar APC ta kasa da ke Abuja a jiya Talata, inda Ganduje ya ce kyawawan ayyukan da Tinubu yake aiwatarwa sun dace domin ci gaban kasar da tattalin arzikinta.

Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da wasu ‘yan Arewa da suka fusata da wasu ‘yan siyasa da suka rasa makama suke kokarin murkushe fatar shugaba Bola Ahmad Tinubu na yin tazarce.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG