Shugaba Muammar Gaddafi na Libya yayi kira ga magoya bayansa da su mike su murkushe 'yan tawayen dake neman kawar da shi daga kan mulki.
A cikin wani gajeren sakon da ya dauka da muryarsa a yau alhamis, shugaba Gaddafi ya bayyana masu yin adawa da shi a zaman beraye, ya kuma yi Allah wadarai da kasashen waje saboda hannun da suka tsoma a wannan rikici.
Wannan jawabi nasa yana zuwa a daidai lokacin da aka barke da kazaminm fada yau alhamis tsakanin masu biyayya ga Gaddafi da 'yan tawaye a wasu unguwanni akalla biyu na Tripoli, babban birnin kasar.
An barke da kazamin fada a Unguwar Abu Salim, inda Gaddafi yake da dimbin magoya baya. Tun fari a yau alhamis, shaidu sun bayarda rahoton jin karar harbe-harben bindigogi a kofar hotel mai suna Corinthia, inda 'yan jarida na kasashen waje da dama suke zaune.
Mayakan 'yan adawa su na ta ci gaba da kwarara zuwa Tripoli domin su taimaka wajen kawar da sauran mayaka masu biyayya ga Gaddafi. Har ila yau, 'yan adawar sun doshi mahaifar Gaddafi, watau garin Sirte. Sojoji masu yin biyayya ga Gaddafi, su na taruwa su ma a garin na Sirte, mai tazarar kilomita 400 a gabas da Tripoli, domin yin arangama da 'yan tawayen.
Ba a dai san inda Gaddafi yake ba a yanzu, amma jami'an gwamnatin Amurka sun ce sun yi imanin har yanzu yana cikin kasar Libya. Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya ambaci wani kakakin gaddafi, Moussa Ibrahim, yana fada yau alhamis cewa shugaban na Libya yana nan cikin koshin lafiya kuma yana jagorancin yakin da ake yi da 'yan tawaye.