Umaru Fintiri wanda shi ne mukaddashin gwamnan jihar a zaben fidda gwamnai da aka yi ya lashe zaben ne da kuri'u 624 inda ya kayar da sauran 'yan takarar da suka hada da Dr Ahmed Muhammed Modibbo wanda ya zo na biyu da kuri'u 197.
'Yan takara irinsu Dr Umar Ardo suna zargin uwar jam'iyyar PDP da nuna son kai ta hanyar bari a yi anfani da sojan gona. Yace sun nunawa shugabannin jam'iyyar cewa bisa ga tsarin mulkin jam'iyyar bai kamata su shiga zabe ba.
Amma an yi kunnen shegu an bari sun shiga zabe. Yace maganar bin doka da oda bata ma cikin harkar dimokradiyar kasar.Bin tsarin mulkin jam'iyyar shi ne kadai zai tabbatar da gaskiya. Idan an bar kowa yayi yadda ya ga dama to kasar zata kasance yadda take yanzu. Za'a ta yin kashe-kashe.
Mukaddashin gwamnan jihar Ahmed Fintiri yace nasarar da ya samu ta mutanen Adamawa ce zaben ma nasu ne. Yace jama'ar jihar sun bukacesu su zo su yi abun da yakamata, su yi masu aiki. Jama'a sun yi masu nasu saura su kuma su yi nasu idan Ubangiji ya basu nasara a zaben wata mai zuwa su cigaba da aikin da suka sa gaba.
Akan ko zai amince da yarjejeniyar da aka yi dashi cewa bayan wannan takarar ba zai sake tsayawa a zaben 2015 ba sai mukaddashin gwamnan yace shi onarebul ne kuma idan an yi yarjejeniya ko a baka ko a tubuce yakamata mutun ya amince da abun da aka yi.
A zaben za'a fafata da jam'iyyar APC da Kowa Party wadda ta fitar da wani manomi Malam Aminu Dahiru. Alhaji Saidu Gwagwai shugaban jam'iyyar a jihar yace sun shirya cewa lallai zasu shiga zaben domin su kawo sauyi a yanayin tafiyar da jihar keyi. Akan ko jam'iyyarsu zata kai labari ganin zata kara da manyan jam'iyyu sai yace mutanen Adamawa wayayyu ne. Sun san yadda suke jefa kuri'arsu. Zasu iya bada mamaki.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.