Jami'an difolomasiyya na Majalisar Dinkin Duniya suna tunanen anfani da matakan tsaro na MDD domin ganin sun mara wa tsarin dakatar da bude wuta a Syria da Amurka da Rashasuka shata, wanda kuma sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry yace wannan it ace hanyar da kawai zai kawo karshen wannan yaki.
Kasar ta Syria dai tana daga yanzu har zuwa tsakiyar ranar gobe jumaa na ta bayyana raayin ta cewa ko tana shiga cikin yarjejeniyar dakatar da bude wuta ko a’a, wanda kuma zai fara aiki ne daga yanzu zuwa gobe.
Kerry yace wani zabi kuma shine iidan Syrian taki amincewa da wannan tsarin, to abin da ka iya faruwa shine kasar zata wargaje, wanda sake komawa kan kafuwan ta abu ne da zaiyi wahala.
Yau din nan dai jamiaan Amurka dana Rasha suna ci gaba da tattaunawa akan yadda za ayi anfani da tsaeri da aka shata na dakatar da bude wuta, abinda mukaddashin ministan harkokin wajen Rasha Mikhail Bagdanov ya bayyana cewa ba wani zabi da ya wuce wanan tsarin.