Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akpabio Ya Musanta Zarge-Zargen Neman Aikata Lalata


Sanata Natasha da Sanata Akpabio
Sanata Natasha da Sanata Akpabio

Shugaban Majalisar Dattawan, wanda yace tun daga 25 ga watan Febrairun daya gabata yake shan kiraye-kirayen waya akan batun, kuma yana sane game da karuwar tattaunawa akan batun a kafafen sada zumunta.

Shugaban Majalisar Dattawan Najerioya Godswill Akpabio ya musanta zargin neman aikata lalata da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ke yi akansa.

Ya yi martanin ne a yau Laraba bayan da Majalisar Dattawan ta koma zamanta, bayan hutun mako guda.

Da yake watsi da zargin, Sanata Akpabio yace, "ban taba cin zarafin wata 'ya mace ba. Na samu tarbiya daga mahaifiyata wacce ta raineni ita kadai, don haka na tashi ina matukar ganin mutuncin 'ya mace. An taba bani kyautar gwamna mafi kula da daidaiton jinsi a Najeriya."

Shugaban Majalisar Dattawan, wanda yace tun daga 25 ga watan Febrairun daya gabata yake shan kiraye-kirayen waya akan batun, kuma yana sane game da karuwar tattaunawa akan batun a kafafen sada zumunta, don haka ya bukaci 'yan Najeriya da kafafen yada labarai da masu amfani da shafukan sada zumunta dasu kaucewa yin hukunci akan batun tare da jiran abinda kotu zata zartar game da shi.

Sabon Korafi

Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta shigar da sabon korafi akan zargin neman aikata lalata da cin amanar mukami akan shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Godswill Akpabio.

Sanata Natasha ta gabatar da korafi karkashin dokar majalisar ta 40, tana zargin shugaban Majalisar Dattawan da neman aikata lalata da kuma cin amanar mukami.

Ta nemi izni domin fitowa ta gabatar da korafin a gaban majalisar a hukumance.

Daga bisani majalisar ta mika korafin ga kwamitinta mai tabbatar da da'a da alfarma da bin dokokin zaman majalisa, inda ta umarce shi ya sake nazari akan batun ba tare da bata lokaci ba.

A watan febrairun daya gabata, cece-kuce ya afkawa majalisar sa'ilin da batun sauya tsarin zama ya rikide zuwa fito na fito tsakanin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da shugaban majalisar dattawan.

Rikici akan tsarin zama ya haifar da zaman tankiya a majalisar dattawan, abinda ya sabbaba zargin neman aikata lalata daga Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, tare da janyo sabuwar damuwa game da kamun kai da tarbiya a zauren majalisar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG