Wannan dokar haramta kungiyar yan uwa Musulmi da ake yiwa lakabi da ‘yan Shi’a da gwamnatin El-Rufai ta yi yanzu haka ya sake bude sabon shafi a game da irin alakar dake akwai a tsakanin wasu kungiyoyin Musulmi, domin yayin da kungiyar Izala ke yabawa daukan wannan mataki, masana shari’a da kuma zaman takewar al’umma gargadi suka yi wa gwamnatocin da ka iya kwaikwayon jihar Kaduna, musamman a wannan lokaci da kasar ke fara murmurewa daga rikicin Boko Haram da kuma wasu tashe tashen hankula da ake fama dasu.
Baya dai ga jihar Kaduna, tuni har wasu jihohin su ka fara kafa dokar hana gangami ko kuma tarukan addini a dai dai lokacin da wasu kungiyoyi ke gudanar da tarukan a shura dake da muhimmanci a Musulunci.
Masana harkar shari’a irinsu Barista Bello Ibrahim Jahun, Malami a tsangayar koyon shari’a da aikin lauya na jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria, na ganin kuskure ne matakan da ake dauka a yanzu.
Kamar Mallam Bello Jahun, shima wani masanin wanda kuma ke ‘daya daga cikin yan kwamitin da gwamnatin jihar Kadunan ta kafa game da tashin hankalin da ya afku a tsakanin sojoji da kungiyar yan uwa Musulmin, Dakta Jibrin Ibrahim, yace kamata yayi gwamnati ta dauki matakan shari’a ba wai haramta wa ‘yan Shi’a gudanar da addininsu ba.