An dade ana zargin batun cewa fannin shari'a a kasar ya dade yana fama da matsalar cin hanci da rashawa.
To sai dai kuma yayin da kungiyar lauyoyi ta kasa ke yin tur da kama alkalan da hukumar tsaro ta farin kaya ta yi, wasu lauyoyin na ganin akwai abin dubawa game da salon yaki da cin hanci da rashawa da gwamnatin kasar ke tutiyar aiwatarwa.
Barista Sunday Joshua Wigra, wani lauya ne mai zaman kansa a Yola, yace da alamun akwai shafaffu da mai a yaki da cin hanci da rashawan.
Shiko wani ‘kusa a kungiyar lauyoyi reshen jihar Taraba, Barista Idris Abdullahi Jalo, na ganin wannan mataki yayi dai dai.
Suma malaman jami’o’i masana shari’a da aikin lauya, na ganin akwai abin dubawa, kamar yadda Mallam Bello Ibrahim Jahun, Malami ne a tsangayar koyon aikin shari’a da lauya na jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria, ke cewa, “akwai bukatar mutunta fannin shari’a, ba wai mutum ba.’’
Da alama dai wannan kame zai ci gaba da jan hankulan masu ruwa da tsaki a fagen shari'ar Najeriya tare da tayar da jijiyoyin wuya a tsakanin lauyoyi, yayin da majalisar sharia ta Najeriya NJC, ke shirin gudanar da wani taron gaggawa kan lamarin.
Saurari rahotan Ibrahim Abdul’aziz.