Belin ya biyo bayan shaidar amsarsu da jami'an DSS suka yi wanda yanzu zai bade babin cigaba da bincike bisa karin alkalai takwas da zai kaiga gurfanar dasu gaban kotu.
Bayanai sun nuna rashin hadin kan hukumar shari'a kan hukumta alkalan wadanda ake zargi da zarmiya ya sanya jami'an DSS kai samame gidajen alkalan.
Banga banga da gwamna Nwike na jihar Rivers yayi wajen hana yin awan gaba da daya daga cikin alkalan daga Fatakwal da ake zargi, ya kara karfafa zargin hadin bakin 'yan siyasa da alkalai a lamuran shari'a a Najeriya.
Alkalai bakwai ne aka bada belinsu wadanda suka hada da Nyang Okoro da Sylvester Nguta na kotun koli da Adeniyi Ademola na babban kotun tarayya Abuja da Kabiru Auta na kotun Kano da Muazu Pindiga na babban kotun Gombe da Muhammad Tsamiya na babban kotun daukaka kara na Ilorin da babban alkalin jihar Enugu Emezulike.
Wani lauya mai zaman kansa Modibo Zakari yace lamarin ba abun mamaki ba ne. Yace kamun ba dole ne ya zama na karshe ba. Yace idan jami'an tsaro suka fara kama mutane biyu ko ukku to lallai akwai wasu da yawa da zasu kama. Kowane alkali yanzu bai san ko an sa masa ido ba kuma ana gap da yin gaba dashi.
To saidai babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta zargi gwamnatin APC da yunkurin murkushe yankin shari'ar kasar.
Keftein Bala Jibril na jam'iyyar APC yace doka daya ce. Babu ta manyan mutane babu kuma ta kananan mutane. Yace abunda aka yiwa alkalan daidai ne kuma shi ne zai nuna cewa kowa da kowa daya suke. Ko shugaban kasa yace idan 'ya'yansa suka sabawa doka a tuhumesu. Yanzu babu sani babu sabo.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.