Rahotanni daga Najeriya na cewa tsohuwar Ministar Kudi, Kemi Adeosun ta fice daga kasar.
Mrs. Adeosun ta fice ne kwana guda bayan da ta yi murabus daga mukaminta, sanadiyar mallakar takardar shaidar yi wa kasa hidima ta NYSC wacce ta kasance ta bogi.
Jaridar yanar gizo ta Premium Times ce ta wallafa labarin a shafinta na yau Asabar, wacce ta ambato wasu majiyoyi wadanda suka tabbatar ta fita kasar waje.
Tun a ranar Juma’a rahotanni suka bayyana cewa Adeosun ta ajiye aikinta bisa wannan dalili, lamarin da fadar shugaban kasa ta tabbatar daga baya.
“A matsayina na wacce ta yi ammana da abin da wannan gwamnati ta saka a gaba na nuna gaskiya, ya kamata na yi abin da ya dace na ajiye aikina.” Adeosun ta bayyana a wasikarta ta murabus, wacce kafafen yada labarai suka wallafa.
Mrs. Adeosun ta fice a kasar ne a daidai lokacin da wasu ke ganin cewa ya kamata a tuhume ta yayin da wasu ke jinjina mata kan matakin da ta dauka.
A Najeriya, ba kasafai ake samun masu rike da madafun iko su sauka daga mukaminsu ba.
An dai kwashe watanni ana ta kiraye-kirayen cewa ya kamata Adeosun ta ajiye aikinta, bayan fitar wani rahoto da jaridar yanar gizo ta Premium Times ta fitar, wanda ke nuna cewa takardarta ta NYSC ta bogi ce.
An haifi tshouwar ministar kudin ta Najeriya a Ingila ne kuma a can ta tashi har ta kammala karatunta.
Bisa ka’ida, duk dan Najeriya da ya kammala karatun digiri ko babbar difloma, sai ya yi wa kasa hidima na tsawon shekara guda - idan mutum bai haura shekaru 30 ba.
Rahotanni sun ce a lokacin da Adeosun ta koma Najeriya tana shekaru 34, lamarin da ya sa ta nemi takardar shaidar a tsame ta daga yin wannan hidimar saboda shekarunta sun haura.
Amma a cewarta, kamar yadda rahotanni suka nuna, ba ta san cewa takardar shaidar da aka ba ta ta bogi ce.
A halin da ake ciki, shugaba Buhari ya nada karamar ministar kudi Zainab Ahmed a matsayin mai rikon kwayar ma’aikatar ta kudi.
Facebook Forum