Yanzu haka wannan guguwar ta hallaka daruruwan mutane a nahityar carribean, ciki harda mutanen kasar Haiti 283 da ta kashe. Izuwa marecen Alhamishin jiya wannan hadarin ya yi karere ne zuwa yammacin tsibirin Bahamas, ya tasar was ashen arewa-maso-yammaci, abinda ke sa ana zaton da safiyar Jumu’ar nan zai dira kan jihar ta Florida.
Ana kiyasta cewa karfin wannan guguwar ya kai maki 4 saboda karfinta, kuma tafe take da iska mai tafiyar kilomita 210 kowace sa’a daya.
Tuni dai shugaban Amurka Barack Obama ya kaddamarda dokar ta-baci a jihohin Florida din da Carolina ta Arewa saboda wannan bala’in da ya abka musu.