Bayan ga batun sake komawa kan teburin shawara da 'yan tawayen, Shugaban Colombia Manuel Santos zai kuma gana da tsohon Shugaban kasar Alvaro Uribe, wanda ya yi nasarar sasanta bangaren adawa da kungiyar ta FARC. Uribe ya gaya ma wani gidan rediyon Colombia cewa a shirye ya ke ya taimaka wajen cimma jituwa da kungiyar ta FARC da kuma kawo karshen yakin da kasar ta shafe shekaru 52 ta na gwabzawa.
Saura kiris masu kada kuri'a su amince da yarjajjeniyar zaman lafiyar da kashi 50.2% akasin 49.7%; wato da rinjayen kuri'u 54,000. Kuri'ar jin ra'ayin jama'a game da zaben raba gardamar na ranar Lahadi ta nuna cewa za a amince da rinjayen daya zuwa biyu.